Kerry ya gana da sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson a jiya Lahadi a birnin London, kwana daya bayan ganawar da ya yi da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da wasu manyan jami’an diplomasiya a birnin Switzerland.
Kerry yace kada wani ya kuskura ya kunna wutar yakin basasa ko kuma ya haddasa rigima tsakanin manyan kasashe biyu masu karfin soja.
Bisa ga dukkan alamu, Kerry yana bayyana damuwansa ne a kan abubuwa dake faruwa a Syria, kama daga matsalolin yan gudun hijira, kisar gillar da ake yiwa fararen hula a birnin Aleppo, hare haren rasha na goyon bayan gwamnatin shugaban kasar Bashar al-Assad, rushewar yarjejeniya da kuma kasawar Amurka wajen kawo karshen zubda jinni da ake yi.
Kerry yayi alkawarin Amurka zata dauki matakin horaswa akan Rasha saboda abubuwan da Rasha din ke myi a garin Aleppo.