A yau Litinin ta bayyanawa manema labarai a Luxembourg cewa babu wata memba da ta nuna bukatar yin hakan.
Mogherini tace an tattauna akan saka takunkumi akan wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Shugaban kasar Syria Bashar Al-Asad, sannan sun jaddada bukatar wadanda suke da hannu a al’amuran dake faruwa a Syria da su samar da hanyar da za’a tattuna domin warware matsalar.
Bayanin nata yazo ne kwana guda a bayan da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yayi gargadi akan yiyuwar saka tankunkumi akan abubuwan da suka shafi Syri, sannan ya fito da kakkausar harshe yana sukar lamirin irin matakan sojan da Rasha take dauka a Syria.
Wannan batu na Syria shine ya kanainaye tattaunawar da shi Kerry yayi jiya lahadi da ministan Harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson da Mnistan Harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da wasu jami'an diflomasiyyar.
A ranar Lahadi Kerry ya bayyana cewa jami’ai sun damu matuka da tashin hankalin da ya sami Arewacin Birnin Aleppo.