Hukumomi sun dade suna neman Gana ruwa a jallo bisa zargin aikata ayyukan ta’addanci a jihar Binuwai da kudancin jahar Taraba.
Kwamandan dake jagorantar rundunar wanzar da zaman lafiya ta hudu da ke Doma a jihar Nasarawa, Manjo Janar Mande Gazama Ali, ya ce rundunar su ta kashe Gana ne a wata musayar wuta a wani shinge da rundunar ta kafa a kan hanya zuwa Makurdi.
Hukumomin suna zargin Akwaza mai lakabin Gana da ayyukan ta’addanci da suka hada da kashe-kashe da satar dabbobi. A can baya dan ta’addan ya kashe jami’an kungiyoyin tsaro da ma sarakunan gargajiya.
Da yake karin haske a kan batun, gwamnan jihar Biniwai Samuel Ortom, a baya ya zargi Akwaza da laifin kai hari a kan wani kauyen da kone musu amfanin gona a wata kasuwar doya, kana daga bisani gwamnatin jihar Binuwai ta yi tayin Naira miliyan goma a kan duk wanda ya ba da bayanai da za su kai ga kamo Akwaza.
Bayan kashe shi, gwamnatin jahar Binuwai ta nuna damuwarta saboda a cewarta, ta bukaci ya zo ne don ta yi masa afuwa da shi da magoya bayansa, bayan da sarakunan jihar suka nemi yin haka domin samun sukin ayukansu.
Gwamnan jihar Binuwai ya nuna rashin jin dadin sa a kan yanda aka kashe Gana a wurin wani taron masu ruwa da tsaki. Ya ce yana jira samun bayanai daga rundunar sojin, kana ya bukaci a sako mutum 40 da aka kama yayin gumuruzun da aka yi kafin kashe Akwaza.
Ga dai rahoton Zainab Babaji daga birnin Jos:
Facebook Forum