Jami'in sadarwa a helkwatar tsaron Najeriya Navy Commander Abdulsalam Sani, ya shaida wa Muryar Amurka cewa dakarun na “Operation Whirl Stroke,” daga bisani sun kara samun bayanan sirri akan wasu ‘yan bindiga da nan take suma suka kai masu farmaki har suka hallaka biyu daga cikinsu kana aka sami nasarar kwato bindigogi kirar gida guda biyu.
A wata fafatawar ta dabam kuma, sojojin sun yi arangama da wasu ‘yan bindigar marigayi Mr. Terwase da kuma ake kira Gana, wanda aka hallaka kwanan baya a jihar Benue. An dai yi wannan fafatawar ne a wani gari da ake kira Sai a karamar hukumar Katsina Ala a jihar Benue, kuma an cafke uku daga cikin ‘yan bindigar tare da kwato wayoyin salula goma sha shida, da layu da kuma miyagun kwayoyi.
Sani ya kara da cewa dakarun sun mamaye wuraren da suka fatattaki 'yan bindigar suna kuma yin sintiri a wurin don tabbatar da cewa tsageran basu koma ba.
A cewar masanin tsaro Farfesa Mohammed Tukur Baba Dan Iyan Mutum Biyu, akwai bukatar gwamnatoci su daina al'adar ba ‘yan ta'adda afuwa muddin ana son shawo kan matsalar tsaro a Najeriya, ya kuma ce ya kamata a hukuntasu.
"Idan aka ci gaba da bada afuwa, a cewarsa to wasu da yawa zasu dauki makamai don daga baya su nemi afuwa."
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:
Facebook Forum