Rundunar 'yan sandan jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya ta kama mutum 51, da take zargi da haddasa rikici a garin Jos, wanda ya kai ga sace dukiyoyin jama'a da daga tutocin kasar Rasha.
Dokar hana zirga-zirgar ta biyo bayan yadda aka ga wasu matasa da suka fito da sunan zanga-zanga, suna kewaye garin Jos da tutoci na kasar Rasha, suna barazana ga mutane da farfasa wasu shaguna da kwashe dukiyar jama'a a Bauchi Road da Zololo Junction da ke cikin kwaryar birnin na Jos.
Wata sanarwa daga sakataren yada labarai na kungiyar JNI a jihar Filato, Sani Mudi, yace Sheihk Muhammad Lawal Adam ya rasu yana da shekaru tamanin a duniya.
Hukumomin tsaro basu tabbatar da harin ba ko adadin wadanda suka rasa ransu da wadanda suka jikkata.
Ayyukan mazabu da 'yan majalisu ke aiwatarwa a shiyyoyin da suke wakilta, su na yin su ne don samar da ci gaban al'umma.
Dalibai biyu ne suka mutu, wassu da dama suka sami raunuka a wani turmutsutsu a jami'ar jahar Nasarawa dake garin Keffi, a gurin neman tallafi.
Shelkwatar rundunar sojin Najeriya da ke Jos, jihar Filato ta gurfanar da wasu jami'anta goma sha bakwai a gaban wata kotu ta musamman, bisa zarginsu da aikata laifukan da suka sabawa tsarin aikinsu.
A kokarin da suke yi na ganin sun samar da tsaro a yankunan jihar Filato da ke fama da tashe-tashen hankula, rundunar sojojin Operation SAFE HAVEN da hadin gwiwan rundunar Operation HAKORIN DAMISA IV sun samu tarwatsa wani wurin kera makamai.
Gamayyar darikun mabiya addinin Kirista sun bukaci hukumomi su samar da tsaro a wuraren da rikici ya shafa a wasu kauyukan jihar Filato, don ba wadanda ke gudun hijira damar sake gina gidajensu su koma.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta dakatar da wani jami'inta mai suna Mr Fred Ogboji, wanda ke kula da karamar hukumar Jos ta Arewa, bisa zargin bacewar wasu muhimman kayayyakin gudanar da zabe.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta cire jami'iyyar PDP a jerin jami'iyyun da zasu shiga zaben da zata gudanar na 'yan majalisun tarayya a shiyyar Arewacin jahar Filato.
Gwamnatin jahar Filato ta sanya dokar hana yawo na awoyi ishirin da hudu a karamar hukumar Mangun jihar Filato.
Domin Kari