Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanarwar Hamas Ta Saba Sharudan Yarjejeniyar Sulhun Gaza – Isra’ila


Kungiyar gwagwarmayar Faladinawa ta Hamas ta sanar da cewa za ta dakatar da musayar mutanen da ta ke garkuwa da su da fursunoni har sai illa masha Allahu a karkashin yarjejeniyar sulhun da ta kulla da Isra’ila.

Isra’ila ta bayyana cewar sanarwar Hamas akan dakatar da gaba ta gaba ta musayar mutanen da take garkuwa dasu da fursunonin Falasdinawa har illa masha allahu ta sabawa gabadayan sharudan yarjejeniyar sulhun Gaza.

A yau Litinin, kungiyar gwagwarmayar Faladinawa ta Hamas ta sanar da cewa za ta dakatar da musayar mutanen da ta ke garkuwa da su da fursunoni har sai illa masha Allahu a karkashin yarjejeniyar sulhun da ta kulla da Isra’ila.

“Za’a daga sakin ‘yan Isra’ilar da ake garkuwa dasu, da aka tsara yi a Asabar mai zuwa, 15 ga watan Febrairun da muke ciki, har sai abinda hali yayi, har sai hukumomin mamayar Isra’ila sun yi biyayya tare da cika alkawuran data dauka makonni da suka gabata,” kamar yadda kakakin dakarun Ezzedine Al-Qassam Brigades, Abu Ubaida, ya bayyana a cikin wata sanarwa.

“Muna jaddada jajircewarmu akan amfani da bangarorin yarjejeniyar matukar ‘yan mamaya suka kiyayesu,” a cewarsa.

Karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila, gabar farko wacce ta fara aiki ranar 19 ga watan Janairun da ya gabata, za'a saki 'yan Isra'ila 33 da aka yi garkuwa da su domin musayar fursunoni 1,900,galibinsu Falasdinawa, da ake tsare dasu gidajen yarin Isra'ila.

A Asabar din data gabata aka kammala musayar wadanda ake garkuwa dasu da fursunoni karo na 5, inda aka saki Yahudawa 3 a madadin Falasdinawa 183.

Da dawowarsu, 73 daga cikin mutane 251 da aka yi garkuwa dasu bayan harin zasu cigaba da zama a Gaza, ciki harda 34 da rundunar sojin Isra'ila tace sun mutu. Sanarwar tace Hamas ta nazarci yadda abokiyar gabarta ta saba ka'idoji da kuma gazawarta wajen kiyaye sharudan yarjejeniyar tsawon makonni 3 da suka gabata".

"Hakan ya hada da jinkirta komawar 'yan gudun hijira zuwa yankin arewacin Gaza, inda aka rika harinsu da makaman atilare da bindigogi a yankuna daban-daban na zirin Gaza, tare da hana nau'ukan kayan agaji wucewa," kamar yadda ta kara da cewar Hamas ta cika dukkanin alkawuran data dauka".

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG