Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Harin Kunar Bakin Wake Ta Kai Wa Rundunar Sojin Pakistan Hari


Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

Wata 'yar harin kunar bakin wake ta afkawa jerin gwanon dakarun da ke taimaka wa rundunar sojin Pakistan a lardin Balochistan da ke fama da rikici a yankin kudu maso yammacin kasar a jiya litinin, inda ta hallaka akalla soja guda tare da jikkata wasu 4, a cewar jami'ai.

"An hallaka akalla daya daga cikin dakarun da ke tsaron kan iyaka tare da jikkata wasu 4 lokacin da wata 'yar harin kunar bakin wake ta kai wa jerin gwanonsu hari a gundumar Kalat," kamar yadda wani babban jami'in gudanarwa Bilal Shabbir ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Haka shima jami'in 'yan sandan yankin Habib Babai, ya tabattar wa AFP adadin wadanda harin ya rutsa dasu.

Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG