Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojojin Pakistan 16 A Kudancin Waziristan


Wasu sojojin Pakistan
Wasu sojojin Pakistan

A ranar Asabar Pakistan ta ruwaito da kisan sojoji akalla 16 a yayin wata arangama da tsagerun yan bindiga a kusa da kan iyakar ta da Afghanistan.

A ranar Asabar Pakistan ta ruwaito da kisan sojoji akalla 16 a yayin wata arangama da tsagerun yan bindiga a kusa da kan iyakar ta da Afghanistan.

Wata sanarwar soji, tace, rikicin da ya afku gabanin wayewar gari, ya faru ne yayin da wasu mayaka dauke da muggan makamai suka afkawa wani karamin ofishin jami’an tsaro dake yankin kudancin Waziristan, a wani hari mafi muni da aka kaiwa dakarun Pakistan a cikin yan watannin baya bayan nan.

Sojoji sunce, mahara 8 suma sun rasa ran su a yayin arangamar.

Sanarwar sojin ta kara da cewa, ana gudanar da aikin tsabtace yankin, kuma wadanda suka aiwatar da mummunar, aika aikar, shakka babu, zasu fuskanci hukunci.

Wani jami’in tsaron Pakistan ya shaidawa muryar Amurka cewa, harin da mayakan su ka kai, ya raunata sojoji 8, kuma da dama da ga cikin sun a cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai. Jami’in ya nemi a a sakaya shi,saboda bas hi da izinin tattauna batun da manema labarai.

Rahotanni sunce, haramtacciyar kungiyar nan ta Tehrik-Taliban Pakistan ko TTP ta dauki alhakin kai mummunan harin, tace, ta kai harin ne, a matsayin ramuwar gayya na kisan wani babban kwamandan ta, a yayin wata arangama da dakarun Pakistan, a farkon makon nan a yankin kusa da garin Tank.

A yayin wani jawabi ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a yayin taron da ta gudanar a makon jiya, Pakistan ta jaddada cewa, TTP da aka sani da Pakistani Taliban, na Shiryo aiyukan ta’addanci ne daga Afghanistan inda suke samun mafaka.

Wakilin Pakistan a Majalisar Dinkin Duniya Usman Iqbal Jadoon yace, Kungiyar ta TTP mai mayaka 6,000, itace kungiya ta baya bayannan da aka sa a jerin kungiyoyin ta’addanci dake gudanar da aiyukan ta a Afghanistan, dake hawa tudun mun tsira a kusa da yankunan kan iyaka, su ka kuma zama kalubale a duk rana ga sha’anin tsaron Pakistan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG