Bayan kammala wani taro na kwanaki biyu da aka yi a birnin tarayya Abuja, Ministan ma’aikatar muhallin Najeriya, Alhaji Ibrahim Usman Jibril ya fadi cewa gwamnatin Najeriya ta amince bisaga manufa, akan wasu muhimman ayyuka da zasu kai ga kammala share dagwalon mai a garin Ogoni dake yankin Niger Delta na Najeriya.
Ministan ya kuma ce sun nemi amincewar majalisa akan wata hukuma dake karkashin ma’aikatar muhalli wadda ke kulawa da abubuwan da suka shafi nau’in abinci da abin sha, da dabbobi, da sauransu, wanda kimiya da fasaha ke sauya yanayinsu don a sami karuwa a kasa.
Alhaji Ibrahim ya kuma ce babban abinda talakan Najeriya zai mora shine an bada kwangilar gyaran hanyar Abuja zuwa Kano akan kudi naira biliyan 155, kuma kamfanin Julius Berger ne zai yi aikin. Hanyar Abuja zuwa Kano na da muhimmanci wajen kawo cigaban tattalin arziki a yankin a cewar ministan. Bayan haka an kuma bada kwangilar gina madatsun ruwa a sassa da bam dabam na kasar.
Ga karin bayani cikin sauti
Facebook Forum