Shekaru tara bayan da wani masanin ilimin na'ura mai kwakwalwa a kasar Japan ya kirkiro da tsarin hada hadar cinikayyar sulalla ko kwandaloli ta kafar manhajar kwamfuta da aka yiwa lakabi da Bitcoin, masana na ci gaba da bincike kan alfanu da kuma kalubalen dake tattare da sabon tsarin, musamman ga al’umar kasashen Afrika, irin su Najeriya.
A shekara ta 2008, aka fara amfani da wannan sabuwar hanyar hada hadar kudi ta Bitcoin a wasu kasashen Asiya dana Turai.
Malam Yusha’u Aliyu, wani mazaunin Abuja na daga cikin mutane kalilan ‘yan Najeriya, dake da masaniya ya bayyana yadda hada hadar ke wakana a cikin wannan kasuwa ta Bitcoin. Ya ce kasuwa ce aka bude a yanar gizo domin kasuwanci daga lokaci zuwa lokaci kuma akan samu riba.
Ko akwai wasu kalubalen nau’ikan kudade da ake hada hadar su wannan kasuwa? Duk da cewa tana gudana ne ta cikin kafar sadarwar intanet Malam Yusha’u Aliyu ya yi karin haske. Inji shi kwandala ce kuma za’a bayanawa mutum darajarta a lokacin da mutum ya saka nashi kudin. Idan darajarta ta karu to mutum ya ci riba. Idan kuma ta fadi, asara ke nan.
Sai dai kamar yadda kowa ya sani, akwai alfanu da kalubale a kowace irin harka ta cinikayya da hada hadar kudi ta duniya. Ita-ma cinikayyar kasuwar Bitcoin, nada nata alfanu da kuma kalubale. Anfanin Bitcoin shi ne yana taimakon mutane su yi kasuwanci ba sai suna wurin ba.
Amma duk da haka malam Yusha’u Aliyu, ya kawo shawara kan matakan da suka kamata hukumomi su dauka domin al’ummar kasashen Afirka irin su Najeriya su ci gajiyar wannan sabuwar fasahar neman arziki ta kafar sadarwar intanet.
Ga Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.
Facebook Forum