Jaridar New York Times ta ce an sayi zanen da sunan Yarima Bader bin Abdullah bin Mohammed bin Farhan al-Saud, amma an san shi babban aboki Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, ne, kuma an san ba ya da wata hanyar samun irin wannan kudi, sannan ba a san shi da tara zane-zane ba. Ba a taba sayen wani zane da tsada haka ba a tarihin duniya.
Zane Mai Suna "Salvator Mundi" ko "Macecin Duniya" Da Ake Zargin Yarima Mohammed bin Salman Da Saya A Kan Kimanin Naira Biliyan 160
- VOA Hausa

1
თეთრი სახლი, ვაშინგტონი, აშშ

2
Wani mutumi yana daukar hoton zanen "Salvator Mundi" na Leonardo da Vinci a gidan gwanjo na Christie's a London, 24 Oktoba, 2017.

3
Wakilan masu son sayen zane-zane suna bayyana mamakinsu a bayan da aka sayi zanen "Salvator Mundi" na Leonardo da Vinci a kan tsabar kudi Dala miliyan 450 (kimanin Naira Biliyan 160) a dakin gwanjon Christie's na New York a ranar laraba 15 Nuwamba 2017.

4
Kwana guda kafin a yi gwanjon zanen "Salvator Mundi" na Leonardo da Vinci, mutane sun yi layi a kofar dakin gwanjon Christie's a New York domin su ganewa idanunsu wannan zane, Talata 14 Nuwamba, 2017.