Miyagun nan da su ka sace wani yaro dan shekaru uku da haihuwa a kofar gidansu, sun fada ragar ‘yan sandan ciki kuma sun fito da yaron lafiya yau.
Da su ke bayanin musabbabin shiga wannan mugun aikin da su ka yi, masu sace mutanen, wadanda matasa ne da su ka hada da Umar Salisu dan shekaru 27 da Jamilu Alasan dan shekaru 30 da kuma Abba Tijjani mai shekaru 17 da haihuwa, sun amsa cewa tsabar son kudi ne ya ingiza su har su ka sace yaron mai suna Suleiman. Su ka ce dukkansu ‘yan unguwar Dawanau ne.
Malam Rabiu Garba shine ya jagoranci tawagar jami’an hukumar ta ‘yan sandan cikin na DSS wajen kama wadannan matasa da kuma ceto yaron da sukayi garkuwa dashi. Y ace bayan da su ka samu labarin abin da ya fari sais u ka tashi haikan wajen ganin sun kamo miyagun. Y ace lashakka miyagun za su gane kurensu. Ya kuma tabbatar da samun yaron cikin koshin lafiya.
Shi kuma mahaifin yaron, Alhaji Ibrahim Suleiman, y ace lokacin da aka gaya masa cewa an ceto dansa ya yi tsammanin mafarki ne yak e yi. Y ace sam bai ba jami’an tsaron ko kwabo ba. Yan a mai cike da godiya ga hukumar ‘yan sandan ciki ta DSS.
Ga dai wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton:
Facebook Forum