Majalisar wakilan Najeriya ta ce sai ta kammala bin diddigin yadda gwamnati ta kashe kudaden da aka ware a cikin kasafin kudin bana domin tsarin nan na samar da ayyuka ga ‘yan Najeriya wato N-Power da kuma baiwa talakawa da marasa karfi naira dubu biyar kowane wata kafin su amince da kudin da aka tanada a kasafin kudin badi.
Hon. Muhammed Ali Wudil ya ce da kwamitin sa zo, ya yi amfani da wani bincike da bankin duniya yayi akan yanki ko jihar da ta fi yawan marasa karfi a Najeriya, abinda ya kawo jinkiri kenan a shirin. Amma duk da haka an riga an fara aiwatar da shirin a wasu jihohin Najeriya tun cikin shekarar da ta gabata.
"Bisa tsarin bada dubu biyar ga marasa karfi, ‘yan gari ko unguwa ne zasu bada fidda yawan wadanda suke gani sun fi talauci a tsakaninsu." a cewar Hon Muhammed. Ya kuma ce biliyan 500 aka ware don wannan shirin tsakanin shekarar da ta gabata wannan shekarar ta 2017.
Shugaban Kwamitin na yaki da fatara ya kuma ce suna bibiyar yadda aka kashe kudaden da aka ware musamman domin wannan shirin. Ya ce amma sun iya gano cewa ba gaba daya ake sakin kudaden shirin ba.
Ga karin bayani cikin rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum