Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu damar ganawa da wasu daga cikin iyayen 'yan matan chibok. A karon farko da ya gana da iyayen a fadar shugaban a babban birnin tarayya Abuja.
Ganawar Shugaba Muhammadu Buhari da Iyayen 'yan matan chibok
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu damar ganawa da wasu daga cikin iyayen 'yan matan chibok.

1
Ministan mata ta Najeriya Hajiya Aisha Alhasan tana ganawa da tawagar 'yan rajin ganin an dawo da 'yan matan makarantar chibok, da 'yan ta'addan Boko Haram suke garkuwa da su. A wata ziyara da suka kai fadar shugaban kasa, a birnin tarayya Abuja ranar 14 ga watan Janairu 2016

2
Shugabar tawagar rajin kwato 'yan matan chibok Oby Ezekwesili da matai makiyar ta Aisha Yesufu, a ziyarar da suka kai fadar shugaban kasa ranar Alhamis Abuja, Najeriya, Janairu 14, 2016.

3
Wasu daga cikin iyayen yaran da 'yan ta'adda suka sace a makarantar Chibok, a wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasar ta birnin tarayya Abuja. ranar Alhamis watan Janaaru 14, 2016.

4
Wasu daga cikin iyayen yaran da 'yan ta'adda suka sace a makarantar Chibok, a wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasar ta birnin tarayya Abuja. ranar Alhamis a watan Janairu 14, 2016.