Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Macron Ya Gabatarwa Trump Wasu Shawarwari Kan Zaman Lafiyar Ukraine


US-FRANCE-POLITICS-DIPLOMACY-TRUMP-MACRON
US-FRANCE-POLITICS-DIPLOMACY-TRUMP-MACRON

Macron na fatan sauya ra’ayin Trump a bikin zagayowar shekara ta 3 da fara yakin Ukraine domin shigar da shugabannin Turai cikin tattaunawar Rasha da Amurka.

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya gana da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Washington a yau Litinin, inda ya gabatar da shawarwarin da za a yi amfani da su wajen magance barazanar Rasha a Turai tare da tabbatar da zaman lafiya a Ukraine.

US-FRANCE-POLITICS-DIPLOMACY-TRUMP-MACRON
US-FRANCE-POLITICS-DIPLOMACY-TRUMP-MACRON

Macron na fatan sauya ra’ayin Trump a bikin zagayowar shekara ta 3 da fara yakin ukraine domin shigar da shugabannin Turai cikin tattaunawar Rasha da Amurka.

Macron ya yi kokarin daidaita irin martanin da kasashen Turai za su mayar akan sauyin manufar bazata da Washington ta yi, inda ya karbi bakuncin ganawa har sau 2 da manyan shugabannin Turai a makon da ya gabata. Rasha “wata barazana ce ga ci gaba da wanzuwar Turai,” kamar yadda ya bayyana a lokacin.

US-FRANCE-POLITICS-DIPLOMACY-TRUMP-MACRON
US-FRANCE-POLITICS-DIPLOMACY-TRUMP-MACRON

“Wannan wata daula ce da ta tarawa kanta makamai kuma ta ke ci gaba da tarawa kanta makamai,” kamar yadda ya bayyana, gabanin ya kama hanyar zuwa Washington.

“Bamu san sanda wannan al’amari zai kare ba a yau. Don haka dole ne muyi maganinsa.”

US-FRANCE-POLITICS-DIPLOMACY-TRUMP-MACRON
US-FRANCE-POLITICS-DIPLOMACY-TRUMP-MACRON

Trump ya yi matukar girgiza Turai sa’ilin da ya bayyana aniyar komawa tattaunawar sulhu da shugaban Rasha Vladimir Putin kuma za a yi tattaunawar ba tare kasashen Turai ko mahukuntan birnin Kyiv ba.

Ya yi ta nanata kalaman Rasha masu ciki da cece kuce na cewar Ukraine ce ta takali yakin, inda ya janyo damuwa a Turai game da cewa zai amince da bangaren yarjejeniyar da Moscow ta tsara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG