Jamus na fama da manyan kalubalen game da tabarbarewar tattalin arziki mafi girma a Turai a tsawon shekaru, tare da matsin lamba na dakile kwararar bakin haure da rashin tabbas kan makomar Ukraine a kawancen ta da Turai da Amurka. Ana sa ran jam’iyar adawa masu ra'ayin mazan jiya ne za suyi nasara a zaben.
Jamus ita ce kasa mafi yawan al'umma a cikin kasashe 27 na Tarayyar Turai kuma babbar memba a kungiyar tsaro ta NATO. Ita ce kuma kasa ta biyu mafi girma dake baiwa Ukraine tallafin makamai, bayan Amurka.
Jamus za ta kasance jigo wajen tsara yadda nahiyar za ta mayar da martani kan kalubalen da ke tattare da yankin shekaru masu zuwa, ciki har da manufofin gwamnatin Trump na tunkarar harkokin waje da cinikayya.
'Yan takarar da ke kan gaba, akwai Friedrich Merz mai ra'ayin mazan jiya da kuma shugaban gwamnati na yanzu Olaf Scholz na jam'iyyar Social Democrats, sun kada kuri'a cikin mintuna kadan da juna a sassa daban-daban na kasar da sanyin safiyar ranar Lahadi.
Dandalin Mu Tattauna