Mako guda bayan mataki da basbbar makarantar horas da lauyoyi ta kasa ta dauka na kin rantsar da wata daliba Musulma bisa hujjar saka hijabi, kungiyoyin Musulmi da kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun yi kira ga makarantar ta hanzarta rantsar da ita, domin kin yin hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kungiyoyin Musulmi na Najeriya sun shirya taron manema labarai karkashin leman Muslim Right Concern, inda suka bayyana cewar kowane dan Najeriya nada yancin yin addininsa kamar yanda dokokin kasa suka gindaya a cikin kundin tsarin mulkin kasar.
Farfesa Ishak Akintola da ya jagorancin jawabai a wurin taron manema labaran, yace abin takaice ganin makarantar da ake horas da lauyoyi wanda zasu kare yancin jama’a amma kuma zai ta zama ta farko da zata take hakkin yan Najeriya, idan kuwa haka ya tabbata, Kenan babu doka da oda a Najeriya.
Barrista Faisal Abubakar wakilin kungiyar lauyoyi Musulmi a wurin taron manema labaran, yace kungiyarsu zata yi rubuce-rubuce har izuwa kotu domin jin dalilin da yasa makarantar ta hanata saka hijabi kuma ji ko shin hakan ya daidai a dokance.
Facebook Forum