Anyi bikin ranar tunawa da sojojin da suka kwanta da dama wato "Memorial Day" wace ake yi a ranar Litinin ta karshe a watan Mayun kowace shekara domin karama wadanda suka mutu a lokacin yaki kuma ranar ta kasance ranar hutu a duk fädin kasar tun shekarar 1971.
Shugaban Amurka Donald Trump Ya Halarci Bikin Tunawa Da Sojojin Da Suka Kwanta Dama

1
Shugaban Amurka Donald Trump ya halarci bikin ranar tunawa da sojojin da suka kwanta dama a makabartar Arlington dake jihar Virginia, ranar 29 ga watan Mayu 2017.

2
Jama'a ta taro dauke da tutar Amurka a filin makabartar Arlington dake jihar Virginia, ranar Lahadi 29 ga watan Mayu 2017.

3
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi jawabi a ranar tunawa da sojojin da suka kwanta dama a makabartar Arlignton dake Jihar Virginia, ran Lahadi 29 ga watan Mayu 2017.

4
Wasu daga cikin tsofin sojojin na kungiyar " Ruck to Remember" sun yi parati a babban filin kasuwanci na birnin Washington, DC, ranar Lahadi 29 ga watan Mayu 2017.
Facebook Forum