Hukuncin umarnin sakin Ibrahim El-Zakzaky ya zone kimanin shekara daya bayan tsare shi da jami’an Najeriya suka yi, biyo bayan arangamar ‘yan kungiyar Shi’a da sojoji a Zaria da hakan ya haddasa asarar rayuka.
Mai shari’a na babbar kotun tarayya Alkali Gabriel Kolawole shine ya bayar da umarnin, bayan ga sakin nasa cikin kwanaki 45, a kuma bashi diyyar Naira Miliyan 50 da kuma gina masa sabon gida a duk inda ya zaba a jahar Kaduna.
Daya daga cikin lauyoyin El-Zakzaky Haruna Magashi, wanda kuma yayi murna da hukuncin yace zabin mallam ne kamar yadda kotu ta bayyana dan gane da inda yakeso ya zauna a gina masa gida.
Shi kuma lauyan hukumar jami’an tsaron asiri DSS Tijjani Gazali, yace zasu nazarci hukuncin don daukar mataki na gaba.
Mai shari’a Gabriel Kolawale dai a hukuncin na sa mai shafi 50 yace babu korafi daga makwabtan El-Zakzaky cewa yana muzguna musu a Zaria. Cikin rahotan kwamitin Shari’a na gwamnatin jahar Kaduna, ya samu jami’an El-Zakzaky da takurawa al’ummar Gillesu a Zaria inda yake gabanin akasin.
Domin Karin Bayani: