Daga cikin rukunin farko na jimlar matasa dubu 200 da zasu ci gajiyar shirin bayar da aiki na N-Power, dubu biyar da doriya ne kadai suka fito daga jahar Kano.
Wasu daga cikin dubban matasa dake jahar Kano sunyi korafi game da wannan batu na daukar aiki. A cewar Abdullahi mai Kano, ba suyi maraba da tsarin gwamnatin tarayya ba kasancewar a Jahar Kano akwai sama da mutane Miliyan 15, amma mutane kalilan aka dauka cikin wannan shirin. Shima Abdurrahman Chali yayi korafi kan wannan tsari inda yayi kira ga ‘yan Majalisun jahar da su dauki mataki.
Yanzu haka dai ‘yan Majalisar Dokoki ta jahar Kano sunce ‘ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa’. Hon. Garba Ya’u Gwarmai wanda ke wakiltar kananan hukumomin Tsanyawa da Kunchi a Jahar, yace abin da yasa ransu ya baci shine yawancin sunayen da aka fitar ba mazauna kananan hukumomin bane.
‘yan Majalisun dai sunce zasu tunkari gwamna domin a tabbatar anbi tsarin bisa ka’ida, a kuma maye gurbin sunayen da aka tabbatar ba mazauna yankunan da suka kamata bane.
Domin karin bayani ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.