Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen da da masana suka bayyana a matsayin kasar da ke fama da wannan matsala, wanda a baya bayan nan aka gano wani salon bautar zamani.
Dabi’ar bautar da dan Adam cikin salon gargajiya wata matsala da ta samu gindin zama shekaru masu yawa a jamhuriyar Nijar. Saboda wasu dalilan da ake dangantawa da al’adu ko na addini lamarin da yasa kungiyoyin fafutuka suka dage don tayar da hukumomi daga barci sai dai kuma har yanzu ana fuskantar turjiya.
Talauci da jahilcin da ake fama da shi a galibin yankunan kasar Nijar na daga cikin dalilan dake mafarin bunkasar sabon salon bautar da masana suka kira bautar zamani, a cewar Hajiya Halima Sarmai kusa a kungiyar yaki da masu gallazawa mata da yara kanana.
Gwamnatin Nijar ta kafa dokar haramta bauta tun a shekarar 2003, amma kuma matsalar ta zamanto tamkar ana hura mata wuta, dalili kenan da kungiyoyin kasa da kasa masu rajin kare hakkin dan Adam suka shawarci gwamnatin da ta sauya salo.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Mumuni Barma.