Kungiyoyi masu nasaba da harkokin sufuri daga sassa daban daban ne suka halarci taron na yini biyu inda kwararru suka gabatar da makala..
Manufar taron ita ce lalubo hanyoyin habaka harkokin sufuri ta yadda zasu dace da zamani musamman a manyan biranen Najeriya irinsu Legas da Abuja da Fatakwal da Kano da Kaduna da dai sauransu.
Za'a cimma manufofin ne ta hanyar samarda dokokin da manufofi da tsare-tsaren da suka kamata.
Tuni kungiyoyin harkokin sufuri a Najeriya suka yi na'am da wannan yunkurin da kudurorin da aka cimma a taron.
Alhaji Sani Sambo Danfulani shugaban kungiyar NATO ta shiyar arewa maso yamma da ta mallaki motocin sufurin Najeriya yace cigaba ne a wajensu. Yace yakamata a yaba masu saboda duk da rashin tsari suna aiki suna iyakar kokarinsu.
Yanzu da sabon tsari ya zo sun rungumeshi saboda shi ne zai ba jama'ar gari jin dadi. Yace waje ne za'a killace. Za'a sa inda mota zata tsaya da lokacin da zata yi a wurin kafin ta tashi. Wanda zai shiga motar zai auna lokacin da zai je da lokacin da zata tashi da lokacin da zai sauka. Za'a kawo motoci ingantattu tare da kebe masu hanyoyin da zasu bi domin gujewa cunkoso.
Yanzu dai gwamnatin jihar Kano ta rabtaba hannu akan wata yarjejeniyar da tayi da wani kamfanin China wanda zai shimfida layin dogo na zamani a wasu sassan birnin Kano wanda zai lakume kudi dalar Amurka biliyan daya da miliyan dari takwas.
Layin dogo da ya taso daga Legas zuwa Abuja zai isa Kano. Amma ana bukatan ya wuje har Katsina zuwa iyaka da Nijar domin habaka kasuwanci.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani