To amma tun ba'a je koina da da shirin sai ga alamun an soma tuki ne da kafar hagu a wasu jihohi inda ake zargin yin cuwa-cuwa a shirin.
Yanzu dai an fara kokawa musamman a wasu jihohin arewa irinsu jihar Neja da Borno da Adamawa da Katsina da Kano da Kebbi da kuma Zamfara.
Mahammad Isuwa na cikin matasan da suka cika takardun shiga aikin ta yanar gizo kamar yadda aka tsara. Yace gaskiyar magana ita ce idan mutum bai kware a yin anfani da naura mai kwakwalwa ba zai samu wahala wajen cike bayanan da ake bukata. Yace abu na biyu kuma shi tushen yanar gizon da shirin yayi anfani dashi ya kan kawo gaddama. Yace shi ya nema ne saboda rashin tsayayyen aiki.
Saidai tuni wasu kungiyoyi suka fara mayarda martani akan yadda ake gudanar da shirin. Onarebul Huseini Gambo Bello daya daga cikin shugabannin kungiyoyin matasan arewa ya koka da cewa su a Adamawa basu san yadda abun yake gudana ba. Yace 'yan kudu sun wawure wuraren.
Malam Garba Shehu kakakin shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari ya musanta zargi. Ya ce abun da ya faru shi ne ana duba yawan masu neman aikin daga kowace jiha. Yace kashi na farko akwai iyakar malaman da za'a ba kowace jiha.Akwai yawan ma'aikatan gona ko na kiwon lafiya da kowace jiha zata samu. Yace idan za'a ba jiha ma'aikatan lafiya kaza amma basu da mutanen da zasu cike gurbin to dole ne a dubi wani fannin daban a yi masu ciko.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.