Malaman na ganin yin hakan zai kawo cigaban da zai taimakawa dalibai wajen fahimtar darusan da suke koya.
Yayinda yake jawabi a wurin wani taron da sashen harsuna da al'adun Afirka na jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria ya shirya Farfasa Munir Mamman dake cikin wadanda suka gabatar da makala a wurin taron yace duk da yake abu ne mai wuya a fara anfani da Hausa a hukumance a Najeriya amma za'a iya farawa da wasu manyan harsuna sannu a hankali.
Yace a halin yanzu abu ne mawuyaci a dauki harshe guda a ce shi ne harshen kasa, sai dai a zabo manya manya guda uku a dinga koyar dasu tun daga firamare har sakandare. Daga nan har zuwa shekaru hamsin ana iya cimma wannan burin.
Dr Sha'aibu Hassan yana daga cikin malaman harsuna da al'adun Afirka na jami'ar Ahmadu Bello yace abun da ake nufi da harshen hukuma shi ne harshen da ake gudanar da ayyuka na gwamnati. Yace idan an je kotu a ce Hausa. Idan an je majalisa ko ta jiha ko ta tarraya a ce Hausa. Idan aka zo tsarin mulki a ce Hausa.
Akwai wasu kasashe da suka yi watsi da harshen mulkin mallaka suka rungumi harshensu kuma sun samu cigaba. Kasashen dake koma baya yau su ne wadanda suke anfani da bakin harsuna.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.