Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Man Dagote Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 890


An sayar da litar Man Fetur akan Naira 320 a Jihar Nasarawa
An sayar da litar Man Fetur akan Naira 320 a Jihar Nasarawa

Saukin farashin da aka samu, ya dace da faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya, sannan, kamfanin na Dangote, yana so talakwan Najeriya suma su ci moriyar saukin farashin da aka samu, domin su samu saukin tsadar rayuwar da ake fama da ita.

Cikin wata sanarwar dauke da sa hannun kakakin kamfanin Dangote Anthony Chiejina kamfanin ya ce, ya rage farashin duk litar man fetur daga ₦950 zuwa ₦890.

Sassaucin da aka samu na ₦60 akan kowacce litar mai ya fara aiki tun daga ranar Asabar din da ta gabata. Sai dai kuma, masana tattalin arziki suna hangen cewa hawa da saukar da farashin man fetur ke yi a kasar, ka iya yiwa masu son zuba hannu jari a kasar kasa a gwiwa.

Wakiliyar Muryar Amurka a Abuja Rukaiya Basha, ta ruwaito cewa bayanan sanarwar kamfanin sun nuna cewa, saukin farashin da aka samu, ya dace da faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya, kuma sanarwar ta kara da cewa, kamfanin na Dangote, yana so talakwan kasar suma su ci moriyar saukin farashin da aka samu, domin samun saukin tsadar rayuwar da ake fama da ita sannan, a daya bangaren kuma, ya bunkasa tattalin arzikin kasar.

A halin da ake ciki yanzu, ‘yan Najeriya suna ci gaba da kokawa akan rashin cin gajiyar sassaucin farashin da ake samu.

Alhaji Zarma Mustapha, shine shugaban sashin gudanarwar na kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu (IPMAN) ya fada wa Muryar Amurka cewa, hada-hadar kasuwancin man fetur ya banbanta da sauran harkokin kasuwanci, domin ba lallai ba ne talakan Najeriya ya more (ji dadi, ci gajiyar, amfana da) saukin farashin da kamfanin man fetur din na Dangote ya sanar ba, kasancewar sai an sayar da man da aka saya akan farashi mai tsada da yake hannu kafin a sayo me saukin da aka samu akan farashi mai sauki.

Zarma ya kara da cewa, yanzu kasuwa ita take yin farashin kanta, don haka babu takamaiman farashi a yanzu.

Sai dai wakiliyar Muryar Amurkar ta ruwaito cewa, wani mai hada-hadar man fetur a Najeriya Sada Dikko, ya ce matakin da kamfanin man Dangote yake dauka na rage farashin man fetur, zai iya tasiri wajen saukaka farashin litar man fetur a kasar.

Sada, ya ce, “kamfanin Dangote ya taimaka wajen fayyace farashin litar man fetur a kasar, ba kamar a baya da kamfanin NNPCL ke sanya farashin man fetur kamar yadda ya ke so ba.

A hirar shi da Muryar Amurka, manazarcin tattalin arziki a jami’ar Usman Danfodiyo dake jihar Sokoto, Dr. Nasir Mainasara, ya ce a mahangar shi, kwan-gaba-kwan-bayan da farashin man fetur ke yi a kasar, ka iya sanyaya gwiwar masu son zuba jari a kasar.

A latsa nan, domin sauraron cikaken rahoton Rukaiya Basha:

Kamfanin Dagote Ya Rage Farashin Litar Man Fetur zuwa #890 -2025-02-02-21-11-29.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG