An kashe dan sanda ne mai shekaru 42 a wajen gidansa da ke birnin Magnanville mai tazarar kilomita 55 daga yammacin birnin Paris, maharin ya kuma shiga gidan ya halaka abokiyar dan sanda, wacce itama tsohuwar jami’ar tsaro ce.
An kuma ceto wani yaro dan shekaru uku a wurin da lamarin ya auku, kana ‘yan sanda sun kashe maharin mai suna Larossi Abballa.
An taba yankewa Abballa, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru uku a shekarar 2013, bayan da aka same shi da laifin daukan mayaka domin zuwa fada a Pakistan.
Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya ce babu haufi harin na ‘yan ta’adda ne.
“Ina so jami’an tsaron Faransa su kwan da sanin cewa, suna da cikakken goyon bayanmu, da kuma duk wata kariya daga cibiyoyin gwamnati.”