Sakatare-Janar din kungiyar kawancen NATO, Jens Stoltenberg ya fadi jiya Litini cewa NATO za ta amince ta girke bataliyoyi hudu na kasa da kasa a Poland da Estonia da Latvia da Lithuania - wadanda su ne kasashen da su ka fi fuskantar barazana daga Rasha.
"Wannan zai aika da sako dalla-dalla na cewa NATO fa a shirye ta ke ta kare duk wata kawarta," a cewar Stoltenbeg a gabanin taron Ministocin Tsaron kasashen da ke cikin kungiyar ta NATO wanda za a fara yau Talata a Brussels, inda ake sa ran jami'ai za su rattaba hannu kan shirin girke sojojin. Stoltenberg ya ce bataliyoyin za su rinka karba-karba ne karkashin jagorancin kwamandojin NATO.
Tattaunawar na aukuwa ne gabanin babban taron NATO da za a yi a Warsaw, kasar Poland a watan Yuli.
Wasu shugabannin kasashen Baltic irinsu Latvia da Lithuania da Estonia, su na cikin fargaba saboda sojojin da NATO ke shirin girkewa ba su da yawan da za su iya sa Rasha ta yi shakkar kai duk wani hari.