Ya zuwa yanzu babu wata kwakkwarar hujja da ke nuna cewa maharin na Orlando na da alaka ta kai-tsaye da kungiyar IS, kuma Darektan hukumar bincike ta FBI, James Comey a jiya Litinin ya ce sun yi imani daga kafar Internet dan bindigar ya samu tsatstsauran ra’ayinsa.
Wani babban jami’i a fannin huldar diplomasiyya a cibiyar Brookings, wato Eric Rosand, ya ce wannan alama ce da ke nuna cewa sakonnin kungiyar ta IS na kaiwa ga dumbin matasan musulmai, wadanda suna wani halin kuncin da za su iya rungumar koyarwar kungiyar ta IS.
A cewar Eric, yanzu ya rage ne ga kowace kasa ta san mafita ga wannan matsala, musamman ta yadda za a ja al’umomin da su ke ganin an ware su a jika.