Ga dukkan alamu, a cewar Obama, yayin da ya ke ganawa da ‘yan jarida a Fadar White House, dan bindigar ya samu bayanai ne daga wadanda ake wallafa a kafar internet.
Obama ya ce, dan bindigar mai suna Omar Saddiqui Mateen mai shekaru 29, wanda kuma aka haifa anan Amurka da iyayensa ‘yan asalin Afghanistan, misali ne na irin ‘yan ta’adda na cikin gida da suke yawan nuna damuwa akansu.
Amma kuma ga dukkan alamu, ya nuna mubaya’arsa ga kungiyar IS a lokacin da ya kira lambar neman daukin gaggawa ta 911.
Fadar White ta sanar da cewa a ranar Alhamis Shugaba Obama zai kai ziyara zuwa birnin na Orlondo.
“ Wannan mummunan hari ne akan Amurkawa, wanda ya kasance mai cin rai musamman ga al’umar Orlando, amma mu san cewa, haka kan iya faruwa a ko’ina a kasar nan, kuma muna goyon bayan al’umar Orlando muna kuma taya iyalan wadanda harin ya rutsa da su alhini.”