Sannan sai canjin yanayi wanda ya zo na biyu a jerin ababan da al’umar nahiyar ke ganin suna masu barazana, yayin da dumbin ‘yan gudun hijra daga Iraqi da Syria ke kwarara zuwa nahiyar a cewar binciken, wanda aka mai taken “Al’umar nahiyar Turai Na Fuskantar Duniya a Rarrabe.”
Bincike har ila yau ya nuna cewa, kashi 17 cikin 100 a kasashen turai goma da aka yi nazarin a kansu, sun nuna cewa kungiyar ta IS tana masu barazana kadan, yayin da kashi uku cikin dari suka nuna cewa kungiyar ba ta barazana ga kasashensu ko kadan.
Hare-haren da aka kai a Paris da Brussels a shekarar da ta gabata, sun sa batun ta’addanci a gaba-gaba a jerin ababan nuna damuwa ga ‘yan nahiyar ta turai, lamarin da ya sa aka kara tsaurara matakana tsaro.
Sai dai mafi yawan ‘yan nahiyar ta turai ba su amince a kara kudaden da ake kashewa ba a fannin soji, saboda a ganinsu daukan matakan soji zai iya kara haifar da kiyayya da tarzoma.