Kan haka ne kungiyar ta Amnesty take kira akan hukumomin na Iraq da su dauki matakan tabattar da ganin an gujewa wannan dabi’a, wacce kungiyar tace ba dalilin yinta.
Amnesty tace ta samu bayanin wadanan abubuwan na faruwa ne daga hirar da ta yi da mutane sunfi 470 da suka hada da irin wadanan mutanen dake tserowa daga yankunan na ISIS, amma kuma sai a cafke su ana zargin su da cewa suna goyon bayan kungiyoyin na ‘yan tsagera.