Rahotanni daga jihar Taraba na nuni da cewa wasu da ba'a san ko su wane ne ba, sun tare hanya inda suka yi awon gaba da wasu matafiya kusan 24 a kan hanyar Takum zuwa Wukari da ke kudancin jihar.
Wasu rahotanni sun bayyana irin shirye-shirye da wasu matasa ke yi na gabatar da bukin sharholiya,
Hadakar kungiyoyin masu bukata ta musamman wato nakasassu a jihar Adamawa sun gudanar da wata zanga zangar lumana domin nuna fushinsu bisa zargin cewa ba a kulawa da su musamman a wannan lokaci na annobar COVID-19, da matsin tattalin arziki da kuma tabarbarewar tsaro.
To a yayin da ake dada ganin rashin burgewar sojojin Najeriya saboda yadda miyagu ke cin karansu ba babbaka a fadin kasar, 'yan sadan sun yaba ma maharba da 'yan sa kai a jahar Adamawa saboda yadda su ka taimaka wajen yaki da miyagu.
Yayin da aka shiga lokacin tunawa da masu fama da cutar kanjamau na zagayen wannan shekarar, abin da ya fi dauke hankali shi ne yadda duniya ke ta mancewa da su saboda raja'ar da aka yi kan batun corona. To sai dai ana ganin bai kamata bukin magaji ya hana na magajiya ba.
Yayin da ake ci gaba da zaman jin bahasi a gaban kwamitocin bincike da aka kafa a jihohi game da zargin cin zarafi da kuma keta hakkin jama'a da ake wa rundunar ‘yan sandan SARS a Najeriya, yanzu haka tuni wasu suka soma bada bahasi.
Biyo bayan kazancewar da wasoson da jama'a ke yi a wuraren ajiye kayayyakin gwamnati, yanzu haka gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya yiwa al'umman jihar jawabi tare da kafa dokar hana fita.
Yayin da ake haramar soma aikin madatsar ruwa ta Mambilla da ake ta cece kuce mahukunta sun gudanar da taron tuntuba da wayar da kan al'umman yankin Mambillan game da aikin da kuma irin hatsarurrukan da za'a iya fuskanta yayin gudanar da wannan aikin.
Matasa a wasu jihohin Najeriya, sun yi ta afkawa rumbunan adand abincin tallafin da gwamnati ta tanada don ragewa mutane radadin annobar coronavirus da ta addabi duniya.
An gudanar da taron wayar da kan jama'a akan muhimancin madatsar ruwa ta Mambila.
Yayin da aka soma girbe amfanin gona, yanzu haka wani batun dake tasowa shine na fadan makiyaya da manoma da Kan jawo asarar rayuka.
Yayin da ake haramar bude makarantu a Najeriya, hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasar NCDC, ta gana da masu ruwa da tsaki don sanin shirin da aka yi, yayin da a nata bangaren Kungiyar Malamai ke nuna damuwarta kan wannan batu.
Yayin da wasu 'yan Najeriya ke yabawa da cigaba da kasancewar Najeriya dunkulalliyar kasa da sauran abuwan cigaba, wasu kuwa na ganin ba ta yi wani cigaba na kirki ba, bayan shekaru 60 da samun 'yancin kai.
Rahotannin daga jihar Taraba na nuni da cewa ana samun kwararar wasu baki da ake zaton mayakan ‘yan awaren kasar Kamaru ne na Ambazonia, lamarin dake haifar da barazanar tsaro a kan iyakar kasashen biyu a cewar rahotannin.
Yayin da ake ci gaba da neman hanyar magance annobar Coronavirus, yanzu matsalar dake addabar jama’a musamman talaka ita ce mawuyacin halin rayuwa, da suka hada da rashin kudi da kuma tsadar rayuwa.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta nuna damuwa game da yadda wasu bata gari kan saje suna sa kayan 'yan Sintiri da na 'yan banga domin yin fashi da kuma ayyukan tu'annati.
Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta samu nasarar bankado mabuyar wasu maza da suka kware wajen yi wa kananan yara mata fyade da kuma lalata su.
Domin Kari