A yau ne ake sa ran cewa ayarin motocin dake dauke da kayan agaji zasu tashi, su tasarwa yankuna daban-daban na kasar Syria wadanda mayakan gwamnati da ‘yantawaye suka tsinke hanyoyin dake zuwa cikinsu, wadanda kuma ke cikin matsananciyar wahalar karancin kayan masrufi na rayuwa.
Wadanan kayan agajin, wandanda suna cikin abubuwan da aka tanada a karkashin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gwamnatin ta Syria da MDD, za’a kai su ne yankuna guda bakwai da suka hada da Madaya da Zabadani dake kusa da babban birnin kasar, da kuma Foua da Kefraya dake lardin Idlib na arewancin kasar.
Manzon MDD a can Syria, Staffan de Mistura, ya fada jiya Talata bayan wani taron da suka yi a birnin Damascus, cewa kai kayan agajin kamar wani gwaji ne na gano ko da gaske gwamnatin Syria ke yi akan alkawarinta na kyale MDD ta rinka kai irin wadanan kayan tallafin ga masu bukatarsu.