Shugabar aiwatar da shirin Malama Turai A .Kadiri ta ce makasudin shirin shine ta ga ta fadada makarantar almajiranta na karatu da ciyarwa ya isa ga yara mata musamman ‘yan gudun hijra da yaran matalauta da yake ba safai ake samun ‘ya mace na almajiranci ba.
Shugabar jami’ra Amurka a Najeriya Dr, Margee Ensign wadda da ta kirkiro shirin ta ce manhajar karatu na shiri ta na karatu da ciyarwa daya yake da na sashin ilimin firamarenta. Ta fada cewa kididdiga ya nuna Najeriya zata zama kasa mafi girma ta uku a duniya nan da 2045, saboda haka kamata ya yi ta tashi tsaye wajen samarwa yara ilimi.
Wani daga cikin wadanda ‘ya’yansa biyu ke cin gajiyar shirin Mal. Dottiwa Adamu ya fada a hirar mu da shi cewa albarkacin wannan shirin, yanzu haka suna karbar karatun boko.
Ga sauran rahoton daga bakin wakilinmu Sanusi Adamu.
Ga karin bayani.