Dr. Babatunde Efayena, yace kamar yadda ya faru ga matar farko wadda ta mutu a sanadiyar kamawa da zazzabin Lassa, itama wannan mata tayi tafiya ne zuwa jihar su ta Kogi, domin bikin aure bayan dawowarta ne ta kama zazzabi wanda ya nuna ta kamu da zazzabin Lassa, amma tana cikin hayyacinta tare da bata kulawa.
Haka kuma an gano cewa matar ta biyu tayi mu’amula da mutanen kimanin sittin, wanda yasa yanzu haka ake sanya idanu akan su. Ita dai matar farko da ta rasu za a yi mata jana’iza kamar yadda hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta tanadar.
Kwamishinan ya bukaci mutane da suyi gaggawar sanar da jami’an kiwon lafiya zarar sun shaida wani mutum yana yin zazzabi mai zafi, kuma su kori duk berayen dake muhallansu.
Domin Karin Bayani.