Wani Malam Ibrahim yace su matasa sun fara ganewa saboda kusan duk 'yan takarar yanzu matasa ne. Mafi yawa matasa ne saboda haka matasan kasar sun waye sun kuma samu cigaba.
Sun gane cewa cutar a keyi idan an zo ana basu kudi su haddasa tashin hankali. Tada rikicin siyasa jahilci ne.
Shi ma Mamman Dauda yace siyasa ba gaba ba ce. Magana ce ta ra'ayi. Kowa ya fadi ra'ayinsa ba fada ba ne. Ya yi kwatanci da yadda kasar ta kunshi kabilu daban daban amma kuma duk 'yan kasa daya ne. Yace haka siyasa take a hukumance. Sun gane siyasa ba gaba ba ce. Babu wanda zasu yi kishi a kansa sai wanda zasu zaba da zai yi masu aiki ba sani ba sabo.
Musa Badamasi yace da sai su dinga bin mutum kawai amma yanzu suna duba abun da muum ya rubuta zai yi. Matasa su duba wanene zai fi cimma muradunsu.
Su matasan ne suka wayar da kawunan 'yanuwansu matasa a duk fadin Nijar. Yanzu babu buge buge balantana kashe kashe. Kowa ya rike akidarshi.
Ga karin bayani.