A yanzu dai kusan kowanne bangare na Najeriya, kayan abinci kamar su Masara da Shinkafa farashin su ya daga, al’amarin da yasa talakawan kasar ke ji a jikinsu.
Tsohon kwamishinan noma a jihar Nija kuma mataimakin shugaban Kwalejin horas da Malamai ta gwamnatin tarayyar Najeriya dake Kwantagora, Alhaji Jibril Dan Wake, yayi karin haske akan dalilin tashin farashin abincin a dai dai wannan lokaci.
Alhaji Jibril yace, abinda ya kawo tashin farashin kayayyakin noma na da yawa saboda wasu sassa na kasar inda Damina batayi musu kyau ba, wasu sassan kuma rikici ya hana su yin noma.
Tuni dai wannan al’amari ya jefa talakawa cikin mawuyacin hali a Najeriyar, wani magidanci mai suna Labaran daga Minna, yace yadda kayayyaki sukayi tsada suna kawai samun abinda zasu ciyar da iyalansu cikin hakuri.
Masana aikin gona na ganin taimakawa kananan manoma da nemo masu zuba jari, zai taimaka wajen samar da abinci a Najeriya da samar da kudaden shiga ga kasar, musammam a dai dai wannan lokaci da kasuwar man fetur ta fadi war war a kasuwannin duniya.
Hukumomin Najeriya sun sha bayyana kokarinsu na bunkasa fannin noma, ko baya ga bullo da shirin bunkasa noman shinkafa na zamani a jihar Jigawa. Itama jihar Nija tace ta banzama cikin duniya wajen nemo masu zuba jari akan noman shinkafa. Noma dai shine tushen arziki inji masu karin magana.
Don karin bayani.