Idan ba'a mantaa ba yayin da yake karbar mulki ya bayyanawa duniya cewa shi nakowa ne amma fa bashi da ubangida ko wani danlele.
Buhari ya soma tabbatar da furucin nasa saboda yawancin wadanda suka sami mukami a gwamnatinsa kawo yanzu ba lallai ne sun taka rawar gani a fafutikar neman zabensa ba. Wasu ma tarihinsu ya nuna 'yan jam'iyyar adawa ta PDP ne.
Alamar tambaya nan ita ce menene ya sa mutane na sha'awar samun mukami a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari? Ko tsohon shugaba Jonathan ya nuna sha'awarsa ta karbar kowane mukami da aka bashi da aka ga ya dace dashi.
Sale Bakuro daga jihar Yobe ya bada amsa. Dalilin da ya sa mutane suna ruruwan shiga gwamnatin Buhari suna yin hakan ne saboda shugaban mai aikata da tsare gaskiya ne. Duk wanda ya yi aiki dashi yana ganin za'a daukeshi mai gaskiya.
Barrister Ibrahim Bello tsohon dan majalisa a karkashi jam'iyyar Buhari ta CPC yace duk wadanda Buhari ya nada yana ganin ba zasu bashi kunya ba. Zasu yi abun da yakamata. Ba zasu bata masa tsarin da ya shirya ba. Gwamnatin Buhari nada alkibla. Duk wanda zai yi aiki yadda aka fada masa Buhari zai nadashi ko daga wacce jam'iyya yake.
Ga karin bayani.