Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabinsa ga shugabannin Afirka da suka hallara a birnin Washington, cewa Amurka za ta iya zama babbar hanyar bunkasa nahiyarsu a shekaru masu zuwa.
A lokacin da Amurka da China da kasashen Yamma ke fafatawa a gasar wa yafi kusanci da kasashen Afirka, shugaban kasar Nijar ya danganta nasarar da China ke samu a Afirka da rashin tsoro.
Taron na mayar da hankali ne kan yadda za a hada kai don bunkasa harkokin cinikayya da saka hannun jari da zai ciyar da tattalin arzikin Afirka gaba don a dama da nahiyar a fagen kasuwancin duniya.
Amurka ta ce za ta sauya yadda take hulda da Afirka, ta yadda sai abin da kasashen nahiyar suke so za a yi.
Shugabannin kasashen Afirka sama da 40 sun hadu a birnin Washington DC don halartar wani muhimmIn taro da shugaban Amurka Joe Biden ya shirya karo na farko tun hawansa mulki.
Masu rajin kare dimokradiya a jamhuriyar Nijer sun yi na’am da taron da ake shirin farawa a yau Talata 13 ga watan disamba a nan birnin Washington DC a tsakanin kasar Amurka da kasashen nahiyar Afirka.
A Najeriya, kwararru a fanin siyasar kasa da kasa da masanan harkokin zamantakewan dan Adam na tafka mahawara akan babban taron Amurka da shugabannin Nahiyar Afirka a daidai lokacin da ake haraman taron a safiyar Talatan nan a birnin Washington D.C.
Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya bi sahun sauran shugabannin Afirka 49 zuwa birnin Washington D.C. domin halartar taron Amurka da shugabannin Afirka, wanda za a fara yau Talata, 13 ga watan Disamba.
A cigaba da kokarin Amurka na kara tasiri a Afurka, wajen bullo da hanyoyin da nahiyar da Amurka za su amfana tare, Amurka ta dukufa wajen ganin cewa taronta da Afurka na wannan karon ya haifar da yarjejeniyoyi masu muhimmanci ga bangarorin biyu. Wannan kuma wata hanya ce ta taka ma China burki.
Gobe Talata ake shirin fara babban taron manyan ‘yan kasuwa da shugabannin kasashen Afirka 49, da kuma kusoshin gwamantin Amurka, ciki har da Shugaba Joe Biden wanda shi zai jagoranci bukin buden taron.
Shugaba Joe Biden na shirin karbar bakuncin shugabannin Afirka da dama a Washington a wannan makon a daidai lokacin da fadar White House ke neman takaita gibin amincewa da Afirka.
Amurka za ta karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka 49 da kuma tawagar kungiyar Tarayyar Afirka a birnin Washington domin halartar taron kwanaki uku na Amurka da Afirka da za a fara ranar Laraba mai zuwa.