Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Taron Amurka da Afurka Kan Cinakayya


Biden Africa Summit
Biden Africa Summit

A cigaba da kokarin Amurka na kara tasiri a Afurka, wajen bullo da hanyoyin da nahiyar da Amurka za su amfana tare, Amurka ta dukufa wajen ganin cewa taronta da Afurka na wannan karon ya haifar da yarjejeniyoyi masu muhimmanci ga bangarorin biyu. Wannan kuma wata hanya ce ta taka ma China burki.

Ajandar babban taron Amurka da kasashen Afurka na nuna cewa za a fi mai da hankali ne kan irin rawar da ‘yan kasuwar Amurka za su taka a nahiyar nan gaba. Akwai ma abin da ake kira, “Zauren Tattauna Harka,” da jami’an Afurka da kamfanonin Afurka a daya bangaren kuma kamfanonin Amurka don tattaunawa da kuma tsara harkokin kasuwanci.

Shugabannin Afurka sama da 40 ne za su halarci taron na kwanaki uku, wanda za a fara ranar Laraba a birnin Washington, yayin da Amurka ke kokarin kara tasirinta a wannan nahiyar wadda muhimmancinta ke karuwa a duniya.

Darren Taylor na dauke da karin bayani.

Bayanan da wasu manyan jami’an Amurka su ka yi sun nuna kwararan bambance bambance tsakanin yadda Amurka ke bullo ma harkar kasuwanci a Afurka, da salon babbar abokiyar gasarta ta fuskar tattalin arziki, wato China.

Mataimakin Sakataren Harkokin Cinakayyar Amurka, Arun Venkataraman ya gaya ma ‘yan jarida a wata hira da su kwanan nan cewa kamfanonin Amurka za su yi harkoki mafiya kyau a Afurka saboda gwamnati ba ta iko da su.

Shugaba Joe Biden
Shugaba Joe Biden

Venkataraman ya ci gaba da cewa, “Ba sun je Afurka ne saboda gwamnatin Amurka na gaya masu su je ko kuma na amincewa su je ba, amma saboda sun lura cewa a matsayinsu na masu hannun jari da fasaha kuma masu zaman kansu, irin bunkasar da Afurka za ta yi cikin gwamman shekaru masu zuwa ya sa nahiyar ta zama wurin da ya dace ka yi harkar kasuwanci muddun ka na so a dama da kai a duniya kuma ka goge. Kuma hakan zai sa kasuwancinsu na hadin gwiwa ya dore ya kuma zama mai haifar da kwakkwaran alfanu na lokaci mai tsawo.”

Venkataraman ya bayyana cewa a shirye kamfanonin Amurka su ke su shiga gogayya da fitaccen kamfanin fasahar China dinnan na Huawei, wanda ya mamaye gurbi mai yawa a fagen lataronin Afurka. Wayar hannun kamfanin da sassanta sun ci kashi 70% na fannin sadarwar 4G na fadin nahiyar.

To amma a wasu kasashe masu tasowa, an hana amfani da kayan fasahar Huawei, saboda fargabar cewa ana amfani da su wajen gudanar da ayyukan leken asiri ma China.

Sakon Venkataraman shi ne, “A yi amfani da kamfanonin Amurka wajen inganta bangaren sadarwa muddun ba a so a damu da batun tsaro a yanar sadarwa.”

Venkataraman ya kara da cewa, “Muddun mu ka yi aiki tare, za mu dada fito da bukatun mutanenmu ta wajen karfafa tsarin sadarwa mara shamaki, wanda aka gina kan tsarin yanar sadarwa mai cike da tsaro, wanda ke kawo azanci da bunkasa, sanayyar kasuwanci da kirkire kirkire, da kuma yanayi na saka jari wanda ke bari a samu bayanai cikin sauki a yayin da kuma yake kare bayanan jama’a.”

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Ya kuma tabbatar cewa Amurka na sha’awar muhimmin ma’adanin nan na “rare earth da Afurka ke da tarinsa, wanda ke da muhimmanci wajen shirye shiryen komawa ga makamashi mai tsafta.”

Masu fashin baki na cewa wannan na nuna yadda gwamnatin Biden ke damuwa da yadda China ke babakere wajen hako wannan muhimmin ma’adani.

Camille Richardson, jami’ar inganta karbuwar Amurka a kasuwannin Afurka da kuma harkokin kasuwanci na hadin gwiwa da Afurka, ta ce nahiyar na dada zama “mai sauyawa bisa ga bukata kuma wuri mai dadin” yin kasuwanci.

Richardson ta ce, “To amma abin da zan ce shi ne, watakila daya daga cikin shingaye mafiya girma ga cinakayya da saka jari a Afurka shi ne rashin madafun harkokin yau da kullum, kuma wannan na daya daga cikin abubuwan da gwamnatin Biden za ta fi mai da hankali kansu. Lashakka batun madafun rayuwa wani bangare ne da mu ke ganin akwai damar hada gwiwa tsakanin gwamnatocinmu da kuma bangarorinmu masu zaman kansu.”

Venkataraman ya nuna cewa a shirye Amurka ta ke ta bayar da kudin gina madafun rayuwa, ciki har da hanyoyin mota, layukan dogo, tasoshin jiragen ruwan da dai sauransu don tallafawa wajen aiwatar da tsarin nan na Cinakayya Mara Shamaki a Nahiyar Afurka.

Wannan saka jari, a cewarsa, zai taimaka wajen kirkiro wata kasuwa guda, ta hadin kai don tabbatar da cewa Afurka na taka muhimmiyar rawa a harkokin kasuwancin duniya.

Richardson kuma ta jaddada cewa wannan babban taron ba zai zama “wajen wage baki kawai ba.”

Birnin Washington daga sama.
Birnin Washington daga sama.

Richardson ta ce, “Za mu rinka yin shelar manyan yarjejeniyoyin da aka cimma akai akai. Mu na so a yi sha’awa da dokin bain. Mu na so zukata da tunanin mutane su koma kai ta yadda lallai za su saka jari a wani sabon kasuwancin hadin gwiwa da Afurka. Kuma labudda za a ji wata sanarwa ta shirin daukar mataki daga wajen Shugaban kasa a karshen wannan babban taron. Abin da zan ce kenan kawai. Yanzu sai a jira zuwa ranar a ji sanarwar.”

Idan zan yi bitar bayanan da su ka gabata, muhimman sakonnin jami’an gwamnatin Biden ga Afurka gabanin wannan babban taro su ne: Kun dade kuna harka da China zuwa yanzu. To amma muddun ku ka ba mu dama, mu ma mu na da abubuwa da yawa da za mu yi ma ku tayinsu, watakila ma fiye da na China. Bangarenmu mai zaman kansa shi ne mafi karfi a duniya, kuma mu na so mu yi harka da mutanen Afurka kan wasu kirkire kirkire wadanda ba kawai kan nahiyar za su yi tasiri ba, amma duniyar baki daya.

Rahoton Darren Taylor daga Johannesburg.

XS
SM
MD
LG