An bude babban taron da Amurka ta shirya da shugabannin kasashen nahiyar Afirka a Washington, babban birnin Amurka a ranar Talata.
Jami’an gwamnatin Joe Biden sun kyankyasa cewa wannan taro, zai bude wani sabon babin kawance tsakanin Amurkar da nahiyar.
Ana kallon nahiyar ta Afirka a matsayin wani yanki da ke da dumbin matasa, walwalar yin kasuwanci da karfin kuri’u a zauren Majalisar Dinkin Duniya, abubuwan da ake ganin za su taimakawa makomar yankin.
Sai dai gabanin fara taron, wani jami’in Amurka ya nuna damuwa kan rashin tabbas ta fuskoki da dama da suka dabaibaye nahiyar.
Ba a dai gayyaci gwamnatocin Burkina Faso, Mali da Sudan ba.
“Saboda mu mutunta matsayar Kungiyar Tarayyar Afirka, ba mu gayyaci wadannan gwamnatoci ba, wadanda aka dakatar da su a kungiyar ta A.U. saboda juyin mulki da aka yi.” In ji Mataimakiyar Sakatare a ofishin Amurka mai kula da sha’anin Afirka Molly Phee.
“Mun fuskanci suka daga wasu, wadanda suke korafi cewa mun gayyaci wannan ko waccar gwamnati da suke da wasu matsaloli. Amma hakan na nuni ne da yadda muka kuduri aniyar ganin an samu fahimtar juna, ko da akwai inda muke da banbancin ra’ayi.” Phee ta ce.
Darekta a majalisar tsaro ta kasa kan sha’anin Afirka, Judd Devermont, ya fadawa manema labarai cewa, gwamnatin Biden ta damu da yadda ake samun “koma baya” a tsarin dimokradiyya musamman a yankin Yammacin Afirka.
“Mun fahimci cewa, idan har muna so a koma kan turbar tsarin mulkin farar hula, sai mun yi tukin-tsaye sosai, musamman wajen ganin mun kulla kyakkyawar alaka da kungiyoyi irinsu ECOWAS da AU da na fararen hula. Saboda haka, a wannan taron koli, za mu tattauna kan hanyoyi da za mu bi wajen ganin mun tabbatar da cewa kasashen na bin tsarin dimokradiyya.” Devermont ya ce.
A cewar Phee, Amurka za ta sake duba yadda za ta sauya huldarta da nahiyar Afirka, ta yadda sai abin da kasashen suke so za a yi, tare da yin la’akkari da irin mummunan tasirin da mulkin mallaka ya yi.
A cewar Phee, “za mu hada kai da Afirka ne ta yadda dukkanmu za mu amfana. Lamarin ba zai zamanto na rige-rige tsakanin manyan kasashen waje ba. Mun fahimci irin mummunan tasiri da tarihi ya nuna. Saboda haka, muna son mu bullowa lamarin cikin mutunci da kuma bin abin da nahiyar ta Afirka ke muradi.”
Ta kara da cewa, gwamnatin Biden, za ta nuna hakan a tattaunawa da za a yi a wannan taron koli, kan makomar shirin nan na AGOA da ke samar da ci gaba ga kasashen Afirka.
“Muna takaicin cewa, ba a ci cikakkiyar moriyar shirin na AGOA yadda ya kamata ba, hakan ya sa muke ganin ya kamata mu dabbaka harkokin kasuwancinmu da Afirka. Za kuma mu duba ko za a ci gaba da shirin ko akasin hakan.”
Phee ta ce babban abin da taron zai mayar da hankali akai shi ne, a tabbatar da cewa an saka abin da ya fi wa nahiyar muhimmanci na samar da ababen more rayuwa.
“Abin da nake hasashe shi ne, taron zai dora kan tattaunawar da Shugaba Biden ya faro a New York yayin taron Majalisar Dinkin Duniya, lokacin da ya yi magana kan muhimmancin samarwa Afirka kujera a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.” Ta kara da cewa.
Taron kolin, zai tabo batutuwan da suka shafi, zaman lafiya, shugabanci, samar da wadataccen abinci, tasirin sauyin yanayi da kasuwanci.
Amma abu muhim da ke ajandar hukumomin Washington shi ne - burin Amurka na zama muhimmiyar kawa ga Afirka.