Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Amurka Da Afirka Zai Kawo Hadin Kan Bangarorin Biyu - Indimi


Tambarin taron shugabannin Amurka da Afirka.
Tambarin taron shugabannin Amurka da Afirka.

Gobe Talata ake shirin fara babban taron manyan ‘yan kasuwa da shugabannin kasashen Afirka 49, da kuma kusoshin gwamantin Amurka, ciki har da Shugaba Joe Biden wanda shi zai jagoranci bukin buden taron.

Wannan taro dai yana da alaka da harkokin kasuwanci, musamman da ya ke Cibiyar Bunkasa Harkokin Kasuwanci ta Amurka wato Corporate Counsel tare da hadin gwiwar gwamnatin Amurka ne suka kira wannan taro.

Manyan baki da Shugabannin Afirka sun fara sauka a birnin Washington D.C, cikinsu har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, da dai sauransu, da suka taho tare da manyan ‘yan kasuwa na kasashen na su.

Daga cikin wadanda su ke cikin tawagar Shugaban Najeriya akwai Shugaban Kamfanin Albarkatun makamashi na Oriental Energy Resources Limited da ke Najeriya, Alhaji Muhammadu Indimi, wanda fitaccen dan kasuwa ne kuma daya daga cikin attajiran Afirka.

A hirarshi da Muryar Amurka, Muhammadu Indimi, ya ce wannan taro ne muhimmi wanda kungiyar manyan kasashe 7 na duniya da suka fi karfin tattalin arziki da ake kira G-7 suka kirkiro.

Riba Da ‘Yan Kasuwa Za Su Samu Da Tsarabar Gwamnatoci

Dangane da ribar da ‘yan kasuwa da gwamnatoci za su iya samu a taron, Indimi ya ce, abu na farko shi ne hada kai. Bisa ga cewar shi, taron wata dama ce ta hada kai. Ya yi misali da yadda yanzu haka Rasha ta ke cikin yaki, kamar yadda Najeriya ta yi fama da Boko Haram da sauransu, ko da yake har yanzu ba a gama ba, amma abun yana lafawa. Yana mai ra’ayin cewa, idan aka hada kai, da manyan kasashen duniya wadannan abubuwan ba za su sake faruwa ba.

Da yake amsa tambayar ko yana gani ‘yan Najeriya suna cin ribar cudanya da Amurka, Indimi ya ce Amurka ta fi bada karfi kan fannin mai a Najeriya, amma duk da haka babu ‘yan kwangilarsu a kasar kamar yadda China ta ke da ‘yan kwangila a Najeriya, duk da yake Amurka ta shiga aikin hakar mai tun lokacin samun ‘yanci kai. Yace, yana yiwuwa man da Amurka ta ke samu ya yi mata kadan.

Ya kuma bayyana cewa, yana da wuya a iya kama China a harkokin kasuwanci a Afirka saboda Chinawa ba su da girman kai, a fannin kasuwanci, da ya sa su ke kananan sana’o'i kamar sayar da burodi da saye da sayarwa a kantuna, sana’o'in da Amurkawa ba za su yi ba.

Faduwar Tattalin Arzikin Kasashen Duniya

Dangane da faduwar tattalin arzikin kasashen duniya kuma, Indimi ya ce ba Najeriya ce kadai ke da matsalar harkokin tattalin arziki ba. Bisa ga cewarshi, Amurka na daya daga cikin kasashen da aka fi bin bashi a duniya. Ya ce bashin da ake bin Najeriya bai taka kara ya karya ba, idan aka kwatanta da basussukan da ake bin sauran kasashen duniya, da ya ce, kowace kasa ta duniya tana fama da shi.

Kan wata rijiyar mai a garin Heglig
Kan wata rijiyar mai a garin Heglig

Samun Mai a Arewacin Najeriya

Da yake tsokaci dangane da fara hakar mai a arewacin Najeriya, Indimi ya ce duk da yake ana bukatar kudi kafin a kai ga samun riba, wannan babban ci gaba ne ainun a yankin kasancewar za a ci moriyar shi ta fannoni da dama da su ka hada da samar da takin noma, da wutar lantarki. Ya kuma bayyana cewa, banda jihohin Bauchi da Gombe da aka kafa tubalin hakar man, akwai mai a jihar Nassarawa da kuma wani bangaren, tafkin Chadi dake jihar Borno, da kuma Bidda da ke jihar Neja. Ya bayyana cewa, idan haka ta tabbata, za a gudanar da ayyukan ne duka a cikin gida domin amfanin gida ba sai an kai waje ba. Bisa ga cewarsa, idan aka sami irin na Bauchi guda uku ko hudu ba za a sake sayo wani abu daga waje ba.

Da yake amsa tambayar ko za su dawo arewa su girke wani abu duk da harkokinsu sun fi karfi a kudu, ya ce yanzu girma yazo musu, amma da yake sun koyar da 'ya'yansu, zabi ya rage wa 'ya'yan da za su gaje su. Ya kuma kara da cewa ‘yan kasuwa za su zo su nemi rijiyoyin mai a arewa, sai dai babbar matsalarsu ita ce rashin tsaro.

Sabbin kudin Naira
Sabbin kudin Naira

Canja Fasalin Naira

Dangane kuma da canza fasalin kudin Najeriya, Muhammadu Indimi ya ce shi bai fahimci tsarin da kuma dalilin wannan canjin sosai ba illa bayanan da hukumomin bankin su ka yi.

Bisa ga cewarshi, kai kudi banki abu ne mai kyau kasancewar mutum ba zai yi fargabar za a yi mashi sata ba, saboda haka, wanan shi ne babban amfanin daukar wannan matakin.

Saurari hirar Indimi da Aliyu Mustapha Sokoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:36 0:00
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG