Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Babban Taron Amurka Ya Karawa Afirka Kima A Idon Duniya


Wasu shugabannin Afirka tare da Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken a wajen taron da Amurka ta shirya a Washington
Wasu shugabannin Afirka tare da Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken a wajen taron da Amurka ta shirya a Washington

Shugabannin kasashen Afirka sama da 40 sun hadu a birnin Washington DC don halartar wani muhimmIn taro da shugaban Amurka Joe Biden ya shirya karo na farko tun hawansa mulki.

Taron kolin na nuna babban yunkurin sake daidaitawa da inganta dangantakar Amurka da kasashe Afirka, wadanda dangantarsu da China da kuma Rasha ke karuwa a baya-bayan nan.

A wannan lokaci da ake ciki, martabar nahiyar Afirka ta karu sosai har a idon manyan kasashen duniya ya kawo kanta, inda ake ganin nahiyar a matsayin yanki mai mumimmanci, tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri a duniya.

Gabanin fara taron kolin, fadar gwamnatin Amurka ta White House ta sanar da shirin zuba jarin dalar Amurka biliyan 55 a fannin tattalin arziki da tsaro da kuma kiwon lafiya a nahiyar Afirka nan da shekaru uku masu zuwa, tare da nada sabon wakili na musamman da zai mai da hankali kan wadannan batutuwa.

A baya-bayan nan dai manyan kasashen duniya da suka hada China da Rasha da Tarayyar Turai da Japan da Turkiyya duk sun gudanar da irin wannan taron kolin da shugabannin Afirka.

Kuma wannan shi ne karo na biyu da Amurka ke karbar bakuncin a cikin shekaru takwas da suka gabata.

A karon farko an kaddamar da taron ne a shekarar 2014 a karkashin shugaba Barack Obama. Har ila yau, ba a bayyana lokacin da na gaba da taron zai kasance ba.

XS
SM
MD
LG