To yayin da ake fama da karancin mai a Najeriyar, shugaban kamfanin mai na kasar-NNPC, Mele Kyari ya bayar da tabbacin cewa mai zai wadata kafin zaben.
Tsohon babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Tukur Buratai, mai ritaya ya bukaci al’ummar kasar su kwantar da hankulan su yana mai bayyana cewa a bisa dukkan matakan tsaron da hukumomin tsaron kasar suka dauka ya zuwa yanzu, za’a gudanar da zaben ranar 25 ga Fabrairu cikin zaman lafiya da lumana.
Ranar Talata 27 ga watan Agusta na shekarar 1991 gwamnatin mulkin soji a Najeriya ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta sanar da kirkiro karin jihohi 9 a kasar, kuma jihar Jigawa na daga cikinsu.
A ranar Juma’a majalisar ta yi wani taron gaggawa don tattauna halin da kasa ke ciki a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar ta PDP a Kano a baya-bayan nan, lamarin da ya sa ta rabu gida biyu tsakanin Wali da Abacha.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, wanda shi zai jagoranci kwamitin ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja.
Hukumar NUC da ke kula da jami’o’in Najeriya ta ba shugabannin jami’o’in kasar umurnin su rufe sai bayan zabe.
Magoya bayan jam'iyun siyasa da za su fafata a zaben da za a gudanar wannan watan sun bayyana dalilansu na marawa jam'iyun baya da kuma dawowa daga rakiyar wadansu.
Tsohuwar jihar Arewa a karkashin Lord Frederick Lugard, ita ce ta koma jihar Arewa ta tsakiya a alif 1967 kafin daga bisani ta zama jihar Kaduna a 1975. A alif 1987 ne kuma aka cire jihar Katsina daga tsohuwar jihar ta Kaduna, wadda a yanzu ke da kananan hukumomi 23.
Hukumomin tsaro a Najeriya, sun ba da tabbacin cewa za a gudanar da zaben 2023 lami lafiya suna masu kore duk wani yunkuri da wasu ke yi musamman a kafafen sada zumunta wajen yada kare-rayi don ganin sun haifar da fargaba a zukatan mutane.
A yayin da ake daf da gudanar da manyan zabuka na shugaban kasa, ‘yan majalisun tarayya, gwamnoni, da na ‘yan majalisun dokokin jihohin kasar 36, akwai muhimman bayanai dabam-daban a kan jihohin Najeriya da irin abubuwan da suka bambanta su da juna.
Domin Kari