A yayin da ake daf da gudanar da manyan zabuka na shugaban kasa, ‘yan majalisun tarayya, gwamnoni, da na ‘yan majalisun dokokin jihohin kasar 36, akwai muhimman bayanai dabam-daban a kan jihohin Najeriya da irin abubuwan da suka bambanta su da juna.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta maida martani kan zargin da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa'i ya yi na cewa wadansu hadiman gwamnati a fadar shugaban kasa suna yi wa jam'iyyar zagon kasa don hana ta samun nasara a zaben da ke tafe.
‘Yan takarar kujerar gwamna a jihar Filato sun sha alwashin magance tarin matsalolin da jihar ke fuskanta in har suka samu nasarar lashe zabe.
A ci gaba da tattaunawarmu da Farfesa Abdulsalam Ya'u Gital game da batutuwan Zabe, ya mana karin haske akan wasu matsaloli da za su iya shafan zabukan dake tafe.
An kuma gano matsaloli da ake samu a wasu wurare na wadandan shekarunsu ba su kai ba, amma suka yi rijistar katin zaben, da kuma wasu da ba ‘yan Najeriya ba da suka yi rijistar yin zabe.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Ahmad Muhammad Bello ya ce su na ilimantar da jami'ai kan sanin dokokin zabe da hakkin dan adam da makamar aiki tare da aiki da doka da oda.
Wasu a birnin Jos na Jihar Filato sun ta’allaka rashin karban katunan na su akan dogon jira da ake yi, yayin da a wasu lokutan kuma ba a samun jami’an hukumar zaben a wuraren da ake raba katunan.
Daga Jihar Bauchi a Najeriyar mun tattauna da Farfesa Abdulsalam Ya'u Gital na jami’ar Abubakat Tafawa Balewa wanda ke bibiyar yadda aikin raba katin zaben ke gudana.
Masana na ci gaba da wayar da kan 'yan Najeriya game da manufofin manyan ‘yan takarar shugabancin kasar, inda suka mayar da hankali kan tabbatar da cewa duk wanda ya yi nasara ya cika alkawuran da ya dauka.
An haifi Mohammed Rabiu Musa da akafi sani da Rabiu Musa Kwankwaso shekaru 67 da suka shude a garin Kwankwaso na karamar hukumar Madobi a jihar Kano Najeriya.
Domin Kari