Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Gwamna: Kotun Daukaka Kara A Kano Ta Ce Wali Ne Dan takarar PDP


Sadiq Wali
Sadiq Wali

Rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar ta PDP a Kano a baya-bayan nan, lamarin da ya sa ta rabu gida biyu tsakanin Wali da Abacha.

Kotun daukaka kara a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta ayyana Sadiq Wali a matsayin dan takarar mukamin Gwamna karkashin jam’iyyar PDP a jihar a zaben da ke tafe a cewar jaridar Daily Trust.

A baya wata babbar kotu ta yanke hukuncin cewa Muhammad Abacha ne dan takarar jam’iyyar ta PDP.

Rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar ta PDP a Kano a baya-bayan nan, lamarin da ya sa ta rabu gida biyu tsakanin Wali da Abacha.

Rahotannin sun yi nuni da cewa, yayin da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Atiku Abubakar yake yakin neman zabensa a Kano a ranar Alhamis, bai daga hannun ko daya daga cikin ‘yan takarar biyu ba.

Bisa al’ada, ya kamata Atiku ya daga hannun dan takarar da za a zaba a mukamin gwamna, amma duba da cewa al’amarin na gaban kotu, sai ya kaucewa yin hakan.

Tun da farko hukumar zabe ta INEC, Wali ta ayyana a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar kafin daga bisani Abacha ya kalubalanci wannan matsaya a kotu.

Sai dai kotun kolin mai alkalai uku da ke Kano, ta yanke hukunci a ranar Juma’ar nan, inda ta ce shugabannin gudanarwar jam’iyyar ta PDP ne kadai ke da hurumin gudanar da zaben fidda gwani.

Sannan duba da cewa Abacha bai tsaya takara a zaben fidda gwanin da shugabannin suka shirya ba, ba shi da ikon ya ce shi ne dan takarar jam’iyyar.

“Muna masu farin ciki da wannan hukunci da kotu ta yanke, sai dai a lokaci guda kuma muna masu bakin ciki saboda rikicin gida da jam’iyyar take fama da shi.

“Saboda haka, abu na farko da za mu yi shi ne, za mu nemi hadin kan dan uwana Muhammad, don mu nemi su zo mu hada kai.” Wali ya ce a wani jawabi da ya yi kai-tsaye wanda gidan rediyon Aminci Radio ya watsa.

XS
SM
MD
LG