Farfesa Mahmood ya kara da cewa, sauyin da aka yi wa dokokin zabe, ya kara saukaka yadda za a gudanar da zaben a zagaye na biyu.
Jamiyyar APC mai mulki ta yi kira ga hukumar EFCC da ICPC da su kama dan takaran kujeran shugaban kasa na jamiyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar akan zargin da aka yi cewa an hada baki da shi an yi sama da fadi da dukiyar al'umman Najeriya.
A yayin da ya rage 'yan makonni a gudanar da babban zabe a Najeriya, wasu daga cikin kananan jam’iyyu a kasar sun bayyana fargaba game da tasirin da kudi zai iya yi a zaben, la’akari da yadda al’amura suka wakana a zabukan da suka gabata a wasu jihohi da ke kasar.
Bisa tsarin dokar zabe da aka yi wa garanbawul a shekarar 2022, alhaki ne akan hukumar ta INEC ta gabatar da rijistar masu zaben ga jam’iyyun.
Tun bayan komawar Najeriya kan tsarin mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999 har ya zuwa yanzu, muhimmin abin da ya fi daukar hankanli shi ne rashin samun wakilcin mata a harkokin siyasa, duk da cewa bincike ya bayyana mafi yawan masu kada kuri’u a ranar zabe mata ne da matasa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar an gudanar da zaben 2023 cikin adalci inda za a damka ragama ga wanda mutane su ka zaba.
‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’yoyi mabanbanta kan goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya sanar.
‘Yan takarar mukamai daban-daban a zaben 2023 na jan hankalin magoya baya wajen ambata alkawuran canji da za su kawo in an ba su dama.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta jaddada kudirinta na aiki tare da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki don dakile yawan amfani da makudan kudade da 'yan siyasa ke yi a lokacin gangamin yakin neman zabe dama sayen kuri’u a lokacin babban zaben kasar mai gabatowa a 2023.
Kungiyar dattawan Arewa ta yi tsokaci kan wani sabon yanayi mai cike da hadari inda wasu ’yan siyasa ke jawo hankalin masu kada kuri’a su sayi katin zabensu na din-din-din a shirye-shiryen zaben 2023 mai zuwa.
Hukumar Zaben Najeriya INEC ta nuna rashin jin dadi game da karancin kasancewar mata a zaben dake karatowa, korafin da mata suka jima suna yi.
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kaddamar da taron yakin neman zaben ta na Arewa maso yammacin Najeriya.
Domin Kari