Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Tabbatar An Gudanar Da Zabe Mai Adalci - Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar an gudanar da zaben 2023 cikin adalci inda za a damka ragama ga wanda mutane su ka zaba.

ABUJA, NIGERIA - Shugaban ya bayyana haka ne a sanarwar sabuwar shekarar nan ta 2023 da a ka shiga a farkon makon nan.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Bayanin ya tabo lamuran kasa da dama kuma shugaban na nuna shekarar ta 2023 na da muhimmanci gare shi da kuma sauran ‘yan Najeriya saboda kokarin da za a yi na zabe da za a samu sake mika mulki ga wata sabuwar gwamnatin farar hula.

Alwashin shugaba Buhari har kullum shi ne zai damka gwamnatin hannun duk wanda ya lashe ko kuma a ce ga duk wanda ‘yan Najeriya su ka zaba.

Ga lamuran tsaro shugaban ya yaba wa dakarun tsaro saboda himmar da su ke yi inda ya ce za a kara ba su kwarin gwiwar aiki don dawo da zaman lafiya mai dorewa.

Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja, Dr. Farouk B. B. Farouk, ya ce yanda kamfen ke gudana na nuna za a iya samun wani sauyi da ba a taba samu a zabukan da aka gudanar a baya ba.

Jami’a a sashen labaru ta hukumar zabe, Zainab Aminu, ta nanata cewa hukumar za ta yi amfani da na’urar tantancewa ta BVAS da za ta hana duk wani yunkurin magudi.

Za a gudanar da babban zaben a ranar 25 ga watan gobe da kuma ranar 11 ga watan Maris na shekarar nan.

Kamfen na ci gaba da gudana tun fara shi a shekarar da ta gabata.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-hikaya:

Za Mu Tabbatar An Gudanar Da Zabe Mai Adalci - Buhari.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

XS
SM
MD
LG