Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a Najeriya, ta ce ta shirya tsaf ko da zaben shugaban kasa zai kai zagaye na biyu.
Shugaban hukumar Farfsesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da jawabinsa a Cibiyar “Chatham House” da ke London a kasar Birtaniya, kan irin shirin da hukumar ta yi don gudanar da zaben 2023.
Chatham House, cibiya ce da ke bincike kan al’amuran da suka shafi manufofin kasashen duniya a fannin siyasa, tattalin arziki, ilimi da shugabanci da sauransu.
“Duk zabukan da muka shirya guda uku a baya, mun shirya tsaf don gudanar da zaben shugaban kasa a zagaye na biyu – ko da hakan za ta faru. In hakan ta faru, ba mu da matsala.” Farfesa Mahmood ya ce.
Farfesa Mahmood ya kara da cewa, sauyin da aka yi wa dokokin zabe a Najeriya, ya kara taimakawa wajen gudanar da zaben a zagayen na biyu cikin sauki.
“An kara tsawaita wa’adin gudanar da zaben na zagaye na biyu, daga mako daya zuwa makonni uku, amma kuma da ma, a ko da yaushe, mu kan zauna cikin shiri ko da hakan za ta faru.” Shugaban hukumar ta INEC ya ce, a lokacin da yake amsa tambayoyi bayan gabatar da jawabinsa.
Shugaban hukumar ya kuma kore batun da wasu ke yadawa cewa za a yi amfani da ma’aikatan kananan hukumomi a maimakon farfesoshi na jami’a a matsayin malaman zabe a jihohi.
“Ba za mu iya amfani da ma’aikatan kananan hukumomi ba, ai ba zaben kananan hukumomi mu ke yi ba, akwai tsari da muke bi, kuma wannan tsari bai sauya ba.” In ji Mahmood.