Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ta Gabatarwa Jam’iyyun Siyasa Rijistar Masu Zabe


Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu
Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu

Bisa tsarin dokar zabe da aka yi wa garanbawul a shekarar 2022, alhaki ne akan hukumar ta INEC ta gabatar da rijistar masu zaben ga jam’iyyun.

A wani taro da ta yi a karon farko a wannan shekara da jam’iyyun siyasar Najeriya, Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta gabatarwa da jam’iyyu 18 rijistar masu zabe.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya gabatar da rijistar a ranar Laraba yayin wannan taro da ya yi da shugabannin jam’iyyun a Abuja.

Bisa tsarin dokar zabe da aka yi wa garanbawul a shekarar 2022, alhaki ne akan hukumar ta gabatar da rijistar zaben ga jam’iyyun.

Jam’iyyun da suka samu halartar zaman sun hada da APC mai mulki, sai babbar jam’iyyar adawa ta PDP da Labour Party sai kuma NNPP da sauran su.

Rijistar da INEC ta gabatarwa jam’iyyun na dauke da bayanan masu kada kuri’a miliyan 93,469,008 wadanda ake sa ran za su kada kuri’a a zaben na 2023.

A ranar 25 ga watan Fabrairu, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, sai kuma a ranar 11 ga watan Maris a gudanar da na gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi.

XS
SM
MD
LG